1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
3 Abokan gābana sun ja da baya;
4 Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi;
5 Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye;
6 Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu,
7 Ubangiji yana mulki har abada;
8 Zai hukunta duniya da adalci;
9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
11 Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona;
12 Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna;
13 Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini!
14 don in furta yabanka
15 Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu;
16 An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa;
17 Mugaye za su koma kabari,
18 Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba,
19 Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara;
20 Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji;