1 Don me, ya Ubangiji, kake tsaya can da nesa?
2 Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi,
3 Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa;
4 Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah;
5 Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara;
6 Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni;
7 Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana;
8 Yakan yi kwanto kusa da ƙauyuka;
9 Yakan yi kwanto a ɓoye kamar zaki.
10 Yakan ragargaza waɗanda suka shiga hannu, su fāɗi;
11 Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta;
12 Ka tashi, Ubangiji! Ka hukunta miyagu, ya Allah.
13 Don me mugun mutum zai ƙi Allah?
14 Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki;
15 Ka karye hannun mugaye da kuma mugun mutum;
16 Ubangiji Sarkin har abada abadin ne;
17 Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala;
18 kana kāre marayu da waɗanda aka danne,