1 Ya mutanena, ku ji koyarwata;
2 Zan buɗe bakina da misalai,
3 abin da muka ji muka kuma sani,
4 Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;
5 Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub
6 don tsara na biye su san su,
7 Ta haka za su dogara ga Allah
8 Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba,
9 Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna,
10 ba su kiyaye alkawarin Allah ba
11 Suka manta da abin da ya aikata,
12 Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu
13 Ya raba teku ya kuma bi da su ciki;
14 Ya bishe su da girgije da rana
15 Ya tsage duwatsu a cikin hamada
16 ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga
17 Amma suka ci gaba da yin masa zunubi,
18 Da gangan suka gwada Allah
19 Suka yi magana a kan Allah,
20 Sa’ad da ya bugi dutse,
21 Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai;
22 gama ba su gaskata ga Allah ba
23 Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa
24 ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci,
25 Mutane suka ci burodin mala’iku;
26 Ya saki iskar gabas daga sammai
27 Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura,
28 Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu,
29 Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su,
30 Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi,
31 fushin Allah ya ƙuna a kansu;
32 Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi;
33 Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza
34 A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi;
35 Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu,
36 Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki,
37 zukatansu ba sa biyayya gare shi,
38 Duk da haka ya kasance mai jinƙai;
39 Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai,
40 Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada
41 Sau da sau suka riƙa gwada Allah;
42 Ba su tuna da ikonsa,
43 ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar
44 Ya mai da kogunansu suka zama jini;
45 Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su,
46 Ya ba da hatsinsu ga fāra,
47 Ya lalace inabinsu da ƙanƙara
48 Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara,
49 Ya saki musu fushinsa mai zafi,
50 Ya shirya hanya wa fushinsa;
51 Ya bugi kowane ɗan fari na Masar,
52 Amma ya fitar da mutanensa kamar garke;
53 Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro;
54 Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki,
55 Ya kori al’ummai a gabansu
56 Amma suka gwada Allah
57 Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci,
58 Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu;
59 Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai;
60 Ya yashe tabanakul na Shilo,
61 Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta,
62 Ya ba da mutanensa ga takobi;
63 Wuta ta cinye matasansu maza,
64 aka karkashe firistocinsu,
65 Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa,
66 Ya kori abokan gābansa;
67 Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf,
68 amma ya zaɓi kabilar Yahuda,
69 Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa,
70 Ya zaɓi Dawuda bawansa
71 daga kiwon tumaki ya kawo shi
72 Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya;