1 Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah?
2 Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa,
3 Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai,
4 Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu;
5 Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura
6 Sun ragargaje dukan sassaƙar katako
7 Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus;
8 Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!”
9 Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba;
10 Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah?
11 Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama?
12 Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa;
13 Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka;
14 Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa
15 Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka;
16 Yini naka ne, dare kuma naka ne;
17 Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya;
18 Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji,
19 Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji;
20 Ka kula da alkawarinka,
21 Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya;
22 Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka;
23 Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka,