1 Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai;
2 Shi kaɗai ne dutsena da cetona;
3 Har yaushe za ku tasar wa mutum guda?
4 Sun kintsa sosai su tumɓuke shi
5 Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;
6 Shi ne kaɗai dutsena da cetona;
7 Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,
8 Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;
9 Talakawa dai kamar shaƙar iska suke,
10 Kada ku dogara a kan ƙwace
11 Abu guda Allah ya ce,
12 kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne.