1 Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji,
2 Ka saurare kukata na neman taimako,
3 Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;
4 Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;
5 Masu fariya ba za su iya tsaya
6 Kakan hallaka masu yin ƙarya.
7 Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma,
8 Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka
9 Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita;
10 Ka furta su masu laifi, ya Allah!
11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;
12 Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai;