1 Ku ji wannan, dukanku mutane;
2 babba da yaro
3 Bakina zai yi maganar hikima;
4 Zan juye kunnena ga karin magana;
5 Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo,
6 waɗanda suka dogara ga arzikinsu
7 Ba wani da zai iya ceton ran wani
8 kuɗin fansa domin rai yana da tsada,
9 da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada
10 Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa;
11 Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada,
12 Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama;
13 Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu,
14 Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari;
15 Amma Allah zai ceci raina daga kabari;
16 Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki
17 gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba,
18 Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne,
19 zai gamu da tsarar kakanninsa,
20 Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba