1 Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana
2 Kai ne mafi kyau cikin mutane
3 Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi;
4 Cikin darajarka ka hau zuwa nasara
5 Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki;
6 Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin;
7 Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta;
8 Dukan rigunanka suna ƙanshin turaren mur da na aloyes, da na kashiya;
9 ’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama;
10 Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne,
11 Sarki ya cika da sha’awar kyanki;
12 Diyar Taya za tă zo da kyauta,
13 Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun;
14 Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki;
15 Aka bi da su cikin farin ciki da murna;
16 ’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka;
17 Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai;