1 Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka
2 Gama kibiyoyinka sun soke ni,
3 Saboda hasalarka babu lafiya a jikina;
4 Laifofina sun mamaye ni
5 Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari
6 An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni;
7 Bayana yana fama da zazzaɓi;
8 Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni;
9 Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji;
10 Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare,
11 Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna;
12 Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu,
13 Ni kamar kurma ne, wanda ba ya ji,
14 Na zama kamar mutumin da ba ya ji,
15 Na dogara gare ka, ya Ubangiji;
16 Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina
17 Gama ina gab da fāɗuwa,
18 Na furta laifina;
19 Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi;
20 Waɗanda suke sāka alherina da mugunta,
21 Ya Ubangiji, kada ka yashe ni;
22 Zo da sauri ka taimake ni,