1 Hikima ba ta yin kira ne?
2 A ƙwanƙoli a kan hanya,
3 kusa da ƙofofin shiga cikin birni,
4 “Gare ku, ya mutane, nake kira;
5 Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali;
6 Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa;
7 Bakina yana magana abin da yake gaskiya,
8 Dukan kalmomin bakina suna da adalci;
9 Ga mai tunani dukansu daidai ne;
10 Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa,
11 gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja,
12 “Ni, hikima, ina zama tare da hankali;
13 Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;
14 Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne;
15 Ta wurina sarakuna suke mulki
16 ta wurina sarakuna suke mulki,
17 Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,
18 Tare da ni akwai wadata da girmamawa,
19 ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla;
20 Ina tafiya a hanyar adalci,
21 ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata
22 “Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa,
23 an naɗa ni tun fil azal,
24 Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni,
25 kafin a kafa duwatsu a wurarensu,
26 kafin ya yi duniya ko gonaki
27 Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu,
28 sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa
29 sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa
30 A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa.
31 ina farin ciki da dukan duniyarsa
32 “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;
33 Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima;
34 Mai albarka ne wanda ya saurare ni;
35 Gama duk wanda ya same ni ya sami rai
36 Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa;