1 Ɗana, ka kiyaye kalmomina
2 Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu;
3 Ka daure su a yatsotsinka;
4 Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,”
5 za su kiyaye ka daga mazinaciya,
6 A tagar gidana
7 Sai na gani a cikin marasa azanci,
8 Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta,
9 da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa,
10 Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi,
11 (Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya,
12 wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali,
13 Sai ta kama shi ta rungume shi
14 “Ina da hadaya ta salama a gida;
15 Saboda haka na fito don in sadu da kai;
16 Na lulluɓe gadona
17 Na yayyafa turare a gadona
18 Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe;
19 Mijina ba ya gida;
20 Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi
21 Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce;
22 Nan take, ya bi ta
23 sai da kibiya ta soki hantarsa,
24 Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;
25 Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta
26 Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci;
27 Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari