Provérbios 6

HAUSA

1 Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi,

2 in maganarka ta taɓa kama ka,

3 to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka;

4 Ka hana kanka barci,

5 Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta,

6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;

7 Ba shi da jagora

8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani

9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?

10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari

12 Sakare da mutumin banza

13 wanda yake ƙyifce da ido,

14 wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa,

15 Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya;

16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,

17 duban reni,

18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,

19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,

20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

21 Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;

22 Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;

23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,

24 suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a

25 Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka

26 Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta,

27 Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa

28 Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi

29 Haka yake da wanda ya kwana da matar wani;

30 Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata

31 Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai

32 Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;

33 Dūka da kunya ne za su zama rabonsa,

34 Gama kishi kan tā da hasalar miji,

35 Ba zai karɓi duk wata biya ba;

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado