Provérbios 5

HAUSA

1 Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata

2 don ka ci gaba da yin kome daidai

3 Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma,

4 amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya,

5 Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa;

6 Ba ta wani tunanin rayuwa;

7 Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;

8 Ku yi nesa da hanyarta,

9 don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu

10 don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku

11 A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi,

12 Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo!

13 Ban yi biyayya da malamaina ba

14 Na zo gab da hallaka gaba ɗaya

15 Ku sha ruwa daga tankinku,

16 In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje,

17 Bari su zama naka kaɗai,

18 Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,

19 Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,

20 Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali?

21 Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji,

22 Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi;

23 Zai mutu saboda rashin ɗa’a

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado