1 Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku;
2 Ina ba ku sahihiyar koyarwa,
3 Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina,
4 ya koya mini ya ce,
5 Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;
6 Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka;
7 Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima.
8 Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka;
9 Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka
10 Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa,
11 Na bishe ka a hanyar hikima
12 Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe;
13 Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce;
14 Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye
15 Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta;
16 Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta;
17 Mugunta da ta’adi
18 Hanyar adali kamar fitowar rana ce,
19 Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne;
20 Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa,
21 Kada ka bari su rabu da kai,
22 gama rai ne ga waɗanda suke nemansu
23 Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,
24 Ka kau da muguwar magana daga bakinka;
25 Bari idanunka su dubi gaba sosai,
26 Ka san inda ƙafafunka suke takawa
27 Kada ka kauce dama ko hagu;