1 Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara.
2 Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun;
3 Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi,
4 Ka tace azurfa
5 ka cire mugaye daga gaban sarki,
6 Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki,
7 gara ya ce maka, “Ka hauro nan,”
8 kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa,
9 In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama,
10 in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka
11 Kalmar da aka faɗa daidai
12 Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla
13 Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi
14 Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama
15 Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki,
16 In ka sami zuma, ka sha isashe kawai,
17 Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka
18 Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini
19 Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa
20 Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi,
21 In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci;
22 Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa,
23 Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama,
24 Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki
25 Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji
26 Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace
27 Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa,
28 Kamar birni da katangarsa sun rushe