1 An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa;
2 Mawadaci da matalauci suna da abu guda.
3 Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka,
4 Sauƙinkai da tsoron Ubangiji
5 A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko,
6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
7 Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci,
8 Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala,
9 Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka,
10 Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje;
11 Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri ne
12 Idanun Ubangiji na lura da sani,
13 Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!”
14 Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi;
15 Wauta tana da yawa a zuciyar yara,
16 Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta
17 Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima;
18 gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka
19 Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji,
20 Ban rubuta maka maganganu talatin ba,
21 ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai,
22 Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta
23 gama Ubangiji zai yi magana dominsu
24 Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai,
25 in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa
26 Kada ka zama mai ɗaukar lamuni
27 gama in ka kāsa biya
28 Kada ka matsar da shaidar kan iyakar
29 Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa?