1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina
2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,
3 in kuma ka kira ga tsinkaya
4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa
5 to, za ka gane tsoron Ubangiji
6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,
7 Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,
8 gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata
9 Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci
10 Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka,
11 Tsinkaya za tă tsare ka,
12 Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane,
13 waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi
14 waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau
15 waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne
16 Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya,
17 wadda ta bar mijin ƙuruciyarta
18 Gama gidanta yana kai ga mutuwa
19 Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa
20 Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki
21 Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar,
22 amma za a fid da mugaye daga ƙasar,