1 Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani,
2 Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji,
3 Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta,
4 Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne,
5 Shirye-shiryen masu adalci daidai ne,
6 Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai,
7 Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu,
8 Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa,
9 Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa
10 Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa,
11 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace,
12 Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane,
13 Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi,
14 Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau
15 Hanyar wawa daidai take a gare shi,
16 Wawa kan nuna fushinsa nan take,
17 Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya,
18 Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi,
19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,
20 Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta,
21 Ba wani lahanin da zai sami masu adalci,
22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,
23 Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa,
24 Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki,
25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,
26 Adali yakan yi hankali a abokantaka,
27 Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta,
28 A hanyar adalci akwai rai;