1 Kaitonki, Ariyel, Ariyel
2 Duk da haka zan yi wa Ariyel kwanto
3 Zan kafa sansani kewaye da ke duka;
4 Za a ƙasƙantar da ke, za ki ƙi yin magana daga ƙasa;
5 Amma abokan gābanki masu yawa za su zama kamar ƙura mai laushi,
6 Ubangiji Maɗaukaki zai zo
7 Sa’an nan sojojin dukan al’umman da suka yi yaƙi da Ariyel,
8 kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci,
9 Ku firgita ku kuma yi mamaki,
10 Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi,
11 Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.”
12 Ko kuwa in kun ba da littafin ga wani wanda ba zai iya karantawa ba, kuka kuma ce, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ban iya karatu ba.”
13 Ubangiji ya ce,
14 Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya
15 Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa
16 Kuna birkitar abubuwa,
17 Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi
18 A wannan rana kurame za su ji maganganun littafi,
19 Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji;
20 Masu zalunci za su ƙare,
21 waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi,
22 Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub,
23 Sa’ad da suka ga ’ya’yansu a tsakiyarsu,
24 Su da suke marasa azanci a ruhu za su sami fahimtar;