1 Ku aiko da raguna a matsayin haraji
2 Kamar tsuntsaye masu firiya
3 “Ku ba mu shawara,
4 Ku bar Mowabawa masu gudun hijira su zauna tare da ku;
5 Da ƙauna za a kafa kursiyi;
6 Mun ji fariyar Mowab,
7 Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi,
8 Gonakin Heshbon sun bushe,
9 Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka,
10 An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya;
11 Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya,
12 Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu,
13 Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab.
14 Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta, ’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”