1 Waɗannan su ne ’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun,
2 Dan, Yusuf, Benyamin, Naftali, Gad da Asher.
3 ’Ya’yan Yahuda maza su ne,
4 Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera.
5 ’Ya’yan Ferez maza su ne,
6 ’Ya’yan Zera maza su ne,
7 ’Ya’yan Karmi maza su ne,
8 Ɗan Etan shi ne,
9 ’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne,
10 Ram shi ne mahaifin Amminadab,
11 Nashon shi ne mahaifin Salma,
12 Bowaz shi ne mahaifin Obed
13 Yesse shi ne mahaifin.
14 na huɗun Netanel,
15 na shidan Ozem
16 ’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel.
17 Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel.
18 Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza.
19 Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur.
20 Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel.
21 Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.
22 Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad.
23 (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.)
24 Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa.
25 ’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne,
26 Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam.
27 ’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne,
28 ’Ya’yan Onam maza su ne,
29 Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid.
30 ’Ya’yan Nadab maza su ne,
31 Ɗan Affayim shi ne,
32 ’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne,
33 ’Ya’yan Yonatan maza su ne,
34 Sheshan ba shi da ’ya’ya maza, sai ’ya’ya mata kawai.
35 Sheshan ya ba da ’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai.
36 Attai shi ne mahaifin Natan,
37 Zabad shi ne mahaifin Eflal,
38 Obed shi ne mahaifin Yehu,
39 Azariya shi ne mahaifin Helez,
40 Eleyasa shi ne mahaifin Sismai,
41 Shallum shi ne mahaifin Yekamiya,
42 ’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne,
43 ’Ya’yan Hebron maza su ne,
44 Shema shi ne mahaifin Raham,
45 Ɗan Shammai shi ne Mawon,
46 Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar
47 ’Ya’yan Yadai maza su ne,
48 Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar
49 Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna
50 Waɗannan su ne zuriyar Kaleb.
51 Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader.
52 Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne,
53 kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.
54 Zuriyar Salma su ne,
55 kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab.