1 Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni,
2 Bari addu’ata ta zo a gabanka;
3 Gama raina yana cike da wahala
4 An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami;
5 An ware ni tare da matattu,
6 Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa
7 Hasalarka tana da nauyi a kaina;
8 Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni
9 idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki.
10 Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne?
11 Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne,
12 An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne,
13 Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji;
14 Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni
15 Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu;
16 Hasalarka ta sha kaina;
17 Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa;
18 Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni;