1 Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini,
2 Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka.
3 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,
4 Ka ba bawanka farin ciki
5 Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji,
6 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji;
7 A lokacin wahala zan yi kira gare ka,
8 A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji;
9 Dukan al’umman da ka yi
10 Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki;
11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji,
12 Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata;
13 Gama ƙaunarka da girma take gare ni;
14 Masu girman kai suna kai mini hari, ya Allah;
15 Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri,
16 Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai;
17 Ka ba ni alamar alherinka,