Salmos 18

HAUSA

1 Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.

2 Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;

3 Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,

4 Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni;

5 Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni;

6 Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;

7 Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza,

8 Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa;

9 Ya buɗe sammai ya sauko;

10 Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya;

11 Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi,

12 daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba,

13 Ubangiji ya yi tsawa daga sama;

14 Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba,

15 Kwarin teku sun bayyana

16 Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni;

17 Ya cece ni daga abokin gābana mai ƙarfi,

18 Sun yi arangama da ni a ranar masifa,

19 Ya fitar da ni zuwa wuri mai sarari;

20 Ubangiji ya yi haka da ni bisa ga adalcina;

21 Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji;

22 Dukan dokokinsa suna a gābana;

23 Na kasance marar laifi a gabansa

24 Ubangiji ya ba ni lada bisa ga adalcina,

25 Ga mai aminci ka nuna kanka mai aminci,

26 ga mai tsabta ka nuna kanka mai tsabta,

27 Kakan cece mai sauƙinkai

28 Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci;

29 Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna;

30 Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce;

31 Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba?

32 Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi

33 Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa;

34 Ya horar da hannuwana don yaƙi;

35 Ka ba ni garkuwar nasara,

36 Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina,

37 Na bi abokan gābana na kuma cim musu;

38 Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba;

39 Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi;

40 Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu,

41 Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba,

42 Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa;

43 Ka cece ni daga harin mutane;

44 da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya;

45 Duk sukan karai;

46 Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena!

47 Shi ne Allah mai sāka mini,

48 wanda yakan cece ni daga abokan gābana.

49 Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji;

50 Yakan ba sarkinsa nasarori;

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado