1 Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi,
2 Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa
3 Ba sa yin wani abin da ba daidai ba;
4 Ka shimfiɗa farillan
5 Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne
6 Da ba zan sha kunya ba
7 Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya
8 Zan yi biyayya da ƙa’idodinka;
9 Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?
10 Na neme ka da dukan zuciyata;
11 Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata
12 Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji;
13 Da leɓunana na ba da labarin
14 Na yi farin ciki da bin farillanka
15 Na yi tunani a kan farillanka
16 Na yi murna a cikin ƙa’idodinka;
17 Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu;
18 Ka buɗe idanuna don in iya gani
19 Ni baƙo ne a duniya;
20 Zuciyata ta ƙosa saboda marmari
21 Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta
22 Ka cire mini ba’a da reni,
23 Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna,
24 Farillanka ne abin farin cikina;
25 An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura;
26 Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini;
27 Bari in gane koyarwar farillanka;
28 Raina ya gaji da baƙin ciki;
29 Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu;
30 Na zaɓi hanyar gaskiya;
31 Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji;
32 Ina gudu a kan hanyar umarnanka,
33 Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka;
34 Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka
35 Ka bi da ni a hanyar umarnanka,
36 Ka juye zuciyata wajen farillanka
37 Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani;
38 Ka cika alkawarinka ga bawanka,
39 Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro,
40 Ina marmarin farillanka ƙwarai!
41 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji,
42 sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina,
43 Kada ka ƙwace maganarka daga bakina,
44 Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka,
45 Zan yi ta yawo a sake
46 Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna
47 gama ina farin ciki da umarnanka
48 Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna,
49 Tuna da maganarka ga bawanka,
50 Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce
51 Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba,
52 Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji,
53 Fushi ya kama ni saboda mugaye,
54 Ƙa’idodinka su ne kan waƙata
55 Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji,
56 Wannan shi ne na saba yi,
57 Kai ne rabona, ya Ubangiji;
58 Na nemi fuskarka da dukan zuciyata;
59 Na lura da hanyoyina
60 Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba
61 Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi,
62 Da tsakar dare nakan tashi in gode maka
63 Ni aboki ne ga duk mai tsoronka,
64 Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji;
65 Ka yi wa bawanka alheri
66 Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau,
67 Kafin in sha wahala na kauce,
68 Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau;
69 Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi,
70 Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi
71 Ya yi kyau da na sha wahala
72 Doka daga bakinka ya fi mini daraja
73 Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni;
74 Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni,
75 Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne,
76 Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya,
77 Bari tausayinka yă zo mini don in rayu,
78 Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili;
79 Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni,
80 Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka,
81 Raina ya tafke da marmari don cetonka,
82 Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka;
83 Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi,
84 Har yaushe bawanka zai yi ta jira?
85 Masu girman kai sun haƙa mini rami,
86 Dukan umarnanka abin dogara ne;
87 Sun kusa gama da ni a duniya,
88 Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka,
89 Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce;
90 Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai;
91 Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau,
92 Da ba don dokarka ce farin cikina ba,
93 Ba zan taɓa manta da farillanka ba,
94 Ka cece ni, gama ni naka ne;
95 Mugaye suna jira su hallaka ni,
96 Ga duk cikakke na ga kāsawa;
97 Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka!
98 Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana,
99 Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina,
100 Ina da ganewa fiye da dattawa,
101 Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya
102 Ban rabu da dokokinka ba,
103 Ɗanɗanon maganarka akwai zaki,
104 Na sami ganewa daga farillanka;
105 Maganarka fitila ce ga ƙafafuna
106 Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi,
107 Na sha wahala sosai;
108 Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji,
109 Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana,
110 Mugaye sun kafa mini tarko,
111 Farillanka su ne gādona har abada;
112 Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka
113 Na ƙi mutane masu baki biyu,
114 Kai ne mafakata da garkuwata;
115 Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta,
116 Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu;
117 Ka riƙe ni za a kuma cece ni;
118 Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka,
119 Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti;
120 Naman jikina na rawan jiki don tsoronka;
121 Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai;
122 Ka tabbatar da lafiyar bawanka;
123 Idanuna sun gaji, da jiran cetonka,
124 Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka
125 Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi
126 Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji;
127 Saboda ina ƙaunar umarnanka
128 saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau,
129 Farillanka masu banmamaki ne;
130 Fassarar maganganunka sukan ba da haske;
131 Ina hakkin da bakina a buɗe,
132 Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai,
133 Ka bi da sawuna bisa ga maganarka;
134 Ka fanshe ni daga mutane masu danniya,
135 Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka
136 Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi,
137 Mai adalci ne kai, ya Ubangiji,
138 Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne;
139 Kishina ya cinye ni ɗungum,
140 An gwada alkawuranka sarai,
141 Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni,
142 Adalcinka dawwammame ne
143 Wahala da damuwa suna a kaina,
144 Farillanka daidai ne har abada;
145 Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji,
146 Na yi kira gare ka; ka cece ni
147 Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako;
148 Ban rufe idanuna ba dukan dare,
149 Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka;
150 Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa,
151 Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji,
152 Tun tuni na koyi daga farillanka
153 Ka dubi wahalata ka cece ni,
154 Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni,
155 Ceto yana nesa da mugaye,
156 Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji;
157 Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini,
158 Na dubi marasa aminci da ƙyama,
159 Dubi yadda nake ƙaunar farillanka;
160 Dukan maganganunka gaskiya ne;
161 Masu mulki suna tsananta mini ba dalili,
162 Ina farin ciki da alkawarinka
163 Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya
164 Sau bakwai a rana ina yabonka
165 Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama,
166 Ina jiran cetonka, ya Ubangiji,
167 Ina biyayya da farillanka,
168 Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka,
169 Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji;
170 Bari roƙona yă zo gabanka;
171 Bari leɓunana su cika da yabonka,
172 Bari harshena yă rera game da maganarka,
173 Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni,
174 Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji,
175 Bari in rayu don in yabe ka,
176 Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya.