1 Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata;
2 Domin ya juye kunnensa gare ni,
3 Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni,
4 Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce,
5 Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci;
6 Ubangiji yana tsare masu tawali’u;
7 Ka kwantar da hankali, ya raina,
8 Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa,
9 don in iya tafiya a gaban Ubangiji
10 Na gaskata, saboda haka na ce,
11 Kuma cikin rikicewana na ce,
12 Yaya zan sāka wa Ubangiji
13 Zan daga kwaf na ceto
14 Zan cika alkawurana ga Ubangiji
15 Abu mai daraja a gaban Ubangiji
16 Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne;
17 Zan yi hadayar godiya gare ka
18 Zan cika alkawurana ga Ubangiji
19 a filayen gidan Ubangiji,