1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,
2 Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa,
3 Saboda wannan ƙasar tana makoki,
4 “Amma kada wani mutum yă kawo tuhuma,
5 Kuna tuntuɓe dare da rana,
6 mutanena suna hallaka saboda jahilci.
7 Yawan ƙaruwar firistoci,
8 Suna ciyar da kansu a kan zunuban mutanena
9 Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke.
10 “Za su ci amma ba za su ƙoshi ba;
11 ga karuwanci,
12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace
13 Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu
14 “Ba zan hukunta ’ya’yanku mata
15 “Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila,
16 Isra’ilawa masu taurinkai ne,
17 Efraim ya haɗa kai da gumaka;
18 Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare,
19 Guguwa za tă share su,