1 Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
2 “In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi?
3 Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana,
4 Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe;
5 Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya;
6 Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba,
7 “Ka duba ka gani yanzu. Wane marar laifi ne ya taɓa hallaka?
8 Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta,
9 A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su,
10 Zakoki suna ruri suna gurnani;
11 Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci,
12 “Asirce aka gaya mini maganan nan,
13 Cikin mafarki da tsakar dare,
14 Tsoro da fargaba suka kama ni
15 Wani iska ya taɓa mini fuska,
16 Ya tsaya cik,
17 ‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci,
18 In Allah bai yarda da bayinsa ba,
19 to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka,
20 Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su;
21 Ba a tuge igiyar tentinsu,