1 Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi.
2 Ayuba ya ce,
3 “A hallaka ranar da aka haife ni,
4 Bari ranan nan ta zama duhu;
5 Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta;
6 Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan;
7 Bari daren yă zama marar amfani;
8 Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana
9 Bari taurarinta na safe su zama duhu;
10 gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina,
11 “Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni,
12 Me ya sa aka haife ni,
13 Da yanzu ina kwance cikin salama;
14 tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa,
15 da shugabanni waɗanda suke da zinariya,
16 Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba,
17 A wurin mugaye za su daina yin mugunta,
18 Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin;
19 Manyan da ƙanana suna a can,
20 “Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci,
21 ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba,
22 waɗanda suke farin ciki
23 Don me aka ba mutum rai,
24 Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci;
25 Abin da nake tsoro ya faru da ni;
26 Ba ni da salama, ba natsuwa;