Isaías 8

HAUSA

1 Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz.

2 Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.”

3 Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz.

4 Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”

5 Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,

6 “Domin wannan jama’a ta ƙi

7 saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu

8 Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta,

9 Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro!

10 Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba;

11 Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce,

12 “Kada ka kira wani abu makirci

13 Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki,

14 zai kuwa kasance a wuri mai tsarki;

15 Yawancinsu za su yi tuntuɓe;

16 Ɗaura shaidar nan ta gargadi

17 Zan saurari Ubangiji,

18 Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona.

19 Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai?

20 Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani.

21 Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu.

22 Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado