1 A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali.
2 A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi.
3 Suna kiran juna,
4 Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.
5 Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”
6 Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade.
7 Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”
8 Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?”
9 Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane,
10 Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe;
11 Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?”
12 sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa
13 Ko da yake kashi ɗaya bisa goma zai ragu a ƙasar,