1 ’Ya’yan Issakar maza su ne,
2 ’Ya’yan Tola maza su ne,
3 Ɗan Uzzi shi ne,
4 Bisa ga tarihin iyalinsu, sun kai mutane 36,000 shiryayyu don yaƙi, gama suna da mata da ’ya’ya da yawa.
5 Dangin da suke maza masu yaƙi sun kasance na dukan gidajen Issakar ne, kamar yadda aka rubuta a cikin tarihi, su 87,000 ne duka.
6 ’Ya’ya uku maza na Benyamin su ne,
7 ’Ya’yan Bela maza su ne,
8 ’Ya’yan Beker maza su ne,
9 Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna da kawunan iyalai da mazan da suka isa yaƙi 20,200.
10 Ɗan Yediyayel shi ne,
11 Dukan waɗannan ’ya’yan Yediyayel maza kawunan iyalai ne. Akwai mazan da suka isa yaƙi waje 17,200.
12 Shuffiyawa da Huffiyawa zuriyar Ir ne, kuma Hushiyawa zuriyar Aher ne.
13 ’Ya’yan Naftali maza su ne,
14 Zuriyar Manasse su ne,
15 Makir ya auri mata daga cikin Huffiyawa da Shuffiyawa. ’Yar’uwarsa ita ce Ma’aka. Wani daga zuriyar, sunansa Zelofehad, shi yana da ’ya’yan mata ne kawai.
16 Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh, ’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem.
17 Ɗan Ulam shi ne,
18 ’Yar’uwarsa Makir mai suna Hammoleket ta haifi Ishod, Abiyezer da Mala.
19 ’Ya’yan Shemida maza su ne,
20 Zuriyar Efraim su ne,
21 Zabad
22 Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya.
23 Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa.
24 ’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce,
25 Refa, Reshef,
26 Ladan, Ammihud,
27 Nun
28 Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta.
29 A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa.
30 ’Ya’yan Asher maza su ne,
31 ’Ya’yan Beriya maza su ne,
32 Heber shi ne mahaifin Yaflet, Shomer da Hotam da kuma ’yar’uwarsu Shuwa.
33 ’Ya’yan Yaflet maza su ne,
34 ’Ya’yan Shemer maza su ne,
35 ’Ya’yan ɗan’uwansa Helem su ne,
36 ’Ya’yan Zofa maza su ne,
37 Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran da Bera.
38 ’Ya’yan Yeter maza su ne,
39 ’Ya’yan Ulla maza su ne,
40 Dukan waɗannan zuriyar Asher ne, kawunan iyalai, zaɓaɓɓun mutane, jarumawa sosai da kuma fitattun shugabanni. Yawan mutanen da suke a shirye don yaƙi, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, 26,000 ne.