1 Zuriyoyin Yahuda su ne,
2 Reyahiya ɗan Shobal shi ne mahaifin Yahat, Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne gidajen Zoratiyawa.
3 Waɗannan su ne ’ya’yan Etam.
4 Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha.
5 Asshur mahaifin Tekowa yana da mata biyu, Hela da Na’ara.
6 Na’ara ta haifi Ahuzzam, Hefer, Temeni da Hawahashtari. Waɗannan su ne zuriyar Na’ara.
7 ’Ya’yan Hela maza su ne,
8 da Koz. Koz ne mahaifin Anub da Hazzobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.
9 Yabez ya fi ’yan’uwansa martaba. Mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, tana cewa, “Na haife shi da azaba.”
10 Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa.
11 Kelub, ɗan’uwan Shuha, shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton.
12 Eshton shi ne mahaifin Bet-Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen Reka.
13 ’Ya’yan Kenaz maza su ne,
14 Meyonotai shi ne mahaifin Ofra.
15 ’Ya’yan Kaleb ɗan Yefunne maza su ne,
16 ’Ya’yan Yahallelel su ne,
17 ’Ya’yan Ezra maza su ne,
18 (Matarsa mutuniyar Yahuda kuwa ta haifi Yared mahaifin Gedor, Heber mahaifin Soko, da kuma Yekutiyel mahaifin Zanowa.) Waɗannan su ne ’ya’yan Bitiya ’yar Fir’auna, wadda Mered ya aura.
19 ’Ya’yan matar Hodiya, ’yar’uwar Naham su ne,
20 ’Ya’yan Shimon maza su ne,
21 ’Ya’yan Shela ɗan Yahuda maza su ne,
22 da Yokim, mutanen Kozeba, da Yowash da Saraf wanda ya yi mulkin Mowab da kuma Yashubi Lehem (Waɗannan rubutattun tarihi ne na tun dā.)
23 Su ne maginan tukwane waɗanda suka zauna a Netayim da Gedera; sun zauna a can suka kuma yi wa sarki aiki.
24 Zuriyar Simeyon su ne,
25 Shawulu ya haifi Shallum, Shallum ya haifi Mibsam. Mibsam ya haifi Mishma.
26 Zuriyar Mishma su ne,
27 Shimeyi yana da ’ya’ya maza goma sha shida da ’ya’ya mata shida, amma ’yan’uwansa ba su da ’ya’ya da yawa; saboda haka gidansu gaba ɗaya ba tă zama mai mutane da yawa kamar mutanen Yahuda ba.
28 Sun zauna a Beyersheba, Molada, Hazar Shuwal,
29 Bilha, Ezem, Tolad
30 Betuwel, Horma, Ziklag,
31 Bet-Markabot, Hazar-Susim, Bet-Biri da Sha’arayim. Waɗannan su ne garuruwansu har lokacin mulkin Dawuda.
32 Ƙauyukan da suke kewayensu su ne Etam, Ayin, Rimmon, Token da Ashan, garuruwa biyar;
33 da kuma dukan ƙauyuka kewaye da waɗannan garuruwa har zuwa Ba’al. Waɗannan ne wuraren zamansu.
34 Zuriyar Simeyon ta ƙunshi Meshobab, da Yamlek,
35 Akwai Yowel,
36 Akwai Eliyohenai da Ya’akoba, da Yeshohahiya,
37 Akwai Ziza ɗan Shifi. Shifi ɗan Allon ne. Allon ɗan Yedahiya ne. Yedahiya ɗan Shimri ne. Shimri kuma ɗan Shemahiya ne.
38 Mutanen da aka jera sunayensu a bisa, shugabannin gidajensu ne.
39 suka tafi bayan garin Gedor wajajen gabashin kwari suna neman makiyaya domin garkunansu.
40 Suka sami makiyaya mai ciyawa mai kyau, ƙasar kuma tana da fāɗi, da salama, kuma zaman lafiya. A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can.
41 Mutanen da aka jera sunayensu sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Suka yaƙi mutanen Ham a wuraren zamansu, haka kuma suka yi da Meyunawa da suke can, suka hallaka su ƙaƙaf, yadda yake har yă zuwa yau. Sa’an nan suka zauna a wurin, gama akwai makiyaya domin garkunansu.
42 Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel, ’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir.
43 Suka karkashe raguwar Amalekawan da suka tsere, suka kuma zauna a can har yă zuwa yau.