Zacarias 5

HAUSA

1 Na sāke dubawa sai ga naɗaɗɗen littafi mai firiya a gabana!

2 Sai ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”

3 Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya.

4 Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ”

5 Sai mala’ikan da yake mini magana ya zo gaba ya ce mini, “Duba ka gani ko mene ne wannan da yake fitowa.”

6 Na tambaya na ce, “Mene ne?”

7 Sa’an nan aka ɗaga murfin dalman, a ciki kuwa ga mace zaune!

8 Ya ce, “Wannan mugunta ce,” ya kuma tura ta cikin kwandon ya rufe da murfin dalman, ya kuma danna da dutse.

9 Na ɗaga idona sama, sai ga mata biyu a gabana, iska tana hura fikafikansu! Suna da fikafikai kamar na shamuwa, suka kuma ɗaga kwandon sama.

10 Na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Ina za ku kai kwandon?”

11 Ya amsa ya ce, “Zuwa ƙasar Babiloniya don a gina masa haikali. Sa’ad da aka gama ginin, za a ajiye shi a ciki.”

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado