1 Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.
2 Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.
3 Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.
4 Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.
5 Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.
6 Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.
7 Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.
8 Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.
9 Sarkin Yeriko, ɗaya
10 sarkin Urushalima, ɗaya
11 sarkin Yarmut, ɗaya
12 sarkin Eglon, ɗaya
13 sarkin Debir, ɗaya
14 sarkin Horma, ɗaya
15 sarkin Libna, ɗaya
16 sarkin Makkeda, ɗaya
17 sarkin Taffuwa, ɗaya
18 sarkin Afek, ɗaya
19 sarkin Madon, ɗaya
20 sarkin Shimron Meron, ɗaya
21 sarkin Ta’anak, ɗaya
22 sarkin Kedesh, ɗaya
23 sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya
24 sarki Tirza, ɗaya.