Jeremias 22

HAUSA

1 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce,

2 ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi.

3 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.

4 Gama in ka lura da bin waɗannan umarnai, to, sarakunan da suke zaune a gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan fada, suna hawan kekunan yaƙi da dawakai, fadawansu da mutanensu suna musu rakiya.

5 Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’ ”

6 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da wannan fadar sarkin Yahuda,

7 Zan aika da mai hallakarwa a kanki,

8 “Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’

9 Amsar kuwa za tă zama, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada suka kuma bauta wa waɗansu alloli.’ ”

10 Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa;

11 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shallum ɗan Yosiya, wanda ya gāji mahaifinsa a matsayin sarkin Yahuda amma bai bar wurin nan ba, “Ba zai ƙara dawowa ba.

12 Zai mutu a inda suka kai shi zaman bauta; ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.”

13 “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci,

14 Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada

15 “Wannan zai mai da kai sarki ne

16 Ya kāre muradin matalauta da mabukata,

17 “Amma idanunka da zuciyarka

18 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda,

19 Za a binne shi kamar jaki

20 “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka,

21 Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya,

22 Iska za tă koro dukan makiyayanka

23 Kai da kake zama a ‘Lebanon,’

24 “Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka.

25 Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa.

26 Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu.

27 Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.”

28 Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya,

29 Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa,

30 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado