1 Da firist nan Fashhur ɗan Immer, babban ma’aikaci a cikin haikalin Ubangiji, ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan abubuwa,
2 sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji.
3 Kashegari, sa’ad da Fashhur ya fitar da shi daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashhur ba, amma ya ba ka suna Magor-Missabib.
4 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi.
5 Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon.
6 Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”
7 Ya Ubangiji, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu;
8 Duk sa’ad da na yi magana, nakan tā da murya
9 Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba
10 Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa,
11 Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi;
12 Ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake gwada adali
13 Ku rera ga Ubangiji!
14 La’ananniya ce ranar da aka haife ni!
15 La’ananne ne mutumin da ya kawo wa mahaifina labari,
16 Bari mutumin ya zama kamar garuruwan
17 Gama bai kashe ni a cikin ciki ba,
18 Me ya sa na ma fito daga cikin ciki