1 Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne.
2 Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba.
3 Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi.
4 Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.
5 Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata.
6 Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce,
7 Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana;
8 Amma ruhun da yake cikin mutum,
9 Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba,
10 “Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni;
11 Na jira sa’ad da kuke magana,
12 na saurare ku da kyau.
13 Kada ku ce, ‘Mun sami hikima;
14 Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba
15 “Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa;
16 Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru,
17 Ni ma zan faɗi nawa;
18 Gama ina cike da magana,
19 a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba,
20 Dole in yi magana in sami lafiya;
21 Ba zan nuna wa wani sonkai ba,
22 gama da a ce na iya daɗin baki,