Hebreus 1

HAUSA

1 A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,

2 amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya.

3 Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.

4 Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.

5 Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa,

6 Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce,

7 Da yake magana game da mala’iku kuwa ya ce,

8 Amma game da Ɗan ya ce,

9 Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta;

10 Ya kuma ce,

11 Su za su hallaka, amma kai kana nan;

12 Za ka naɗe su kamar mayafi,

13 Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa,

14 Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado