Ezequiel 30

HAUSA

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

2 “Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

3 Gama ranar ta yi kusa,

4 Takobi zai zo a kan Masar,

5 Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.

6 “ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa,

7 Za su zama kango

8 Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji,

9 “ ‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo.

10 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

11 Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai,

12 Zan kafe rafuffukan Nilu

13 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

14 Zan lalace Masar ta Bisa

15 Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,

16 Zan ƙuna wuta wa Masar;

17 Samarin Heliyofolis da Bubastis

18 Duhu ne zai zama rana a Tafanes

19 Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar,

20 A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

21 “Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi.

22 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa.

23 Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.

24 Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa.

25 Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar.

26 Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado