1 Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,
2 “Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,
3 Ubangiji mai yaƙi ne
4 Karusan Fir’auna da sojojinsa
5 Zurfafan ruwaye sun rufe su;
6 Hannun damanka, ya Ubangiji,
7 “A cikin girman kwarjininka
8 Da hucin numfashin hancinka
9 Magabci ya yi fahariya, cewa
10 Amma ka hura numfashinka
11 Wane ne cikin alloli,
12 “Ka miƙa hannunka na dama,
13 A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe
14 Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki
15 Sarakunan Edom za su tsorata,
16 Razana da tsoro za su fāɗo a kansu.
17 Za ka kawo su, ka dasa su
18 “Ubangiji zai yi mulki
19 Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.
20 Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.
21 Miriyam ta yi musu waƙa.
22 Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.
23 Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara).
24 Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”
25 Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi.
26 Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
27 Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.