2 Samuel 23

HAUSA

1 Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe.

2 “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina;

3 Allah na Isra’ila ya yi magana,

4 yana kama da hasken safiya

5 “Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba?

6 Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan

7 Duk wanda ya taɓa ƙaya

8 Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda.

9 Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu,

10 amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.

11 Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa.

12 Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.

13 A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.

14 Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.

15 Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”

16 Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.

17 Sai ya ce, “Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba.

18 Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.

19 Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.

20 Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.

21 Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin.

22 Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku.

23 Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

24 Cikin talatin ɗin kuwa akwai,

25 Shamma, mutumin Harod,

26 Helez, mutumin Falti,

27 Abiyezer, mutumin Anatot, da

28 Zalmon, mutumin Aho,

29 Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa,

30 Benahiya, mutumin Firaton,

31 Abi-Albon, mutumin Arba, da

32 Eliyaba, mutumin Sha’albo,

33 ɗan Shamma mutumin Harar,

34 Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka,

35 Hezro, mutumin Karmel,

36 Igal, ɗan Natan mutumin Zoba,

37 Zelek, mutumin Ammon

38 Ira, mutumin Itra.

39 da kuma Uriya, mutumin Hitti.

Ler em outra tradução

Comparar lado a lado