1 Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah.
2 Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji.
3 Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.
4 Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
5 Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,
6 Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.
7 A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.
8 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa;
9 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
10 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki
11 Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
12 Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata,
13 Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa,
14 Shi ne Ubangiji Allahnmu;
15 Yakan tuna da alkawarinsa har abada,
16 alkawarin da ya yi wa Ibrahim
17 Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida,
18 “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana
19 Sa’ad da suke kima,
20 suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma,
21 Bai bar wani ya zalunce su ba;
22 “Kada ku taɓa shafaffuna;
23 Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka;
24 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
25 Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo;
26 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,
27 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;
28 Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai,
29 ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa.
30 Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka!
31 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
32 Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri;
33 Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,
34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
35 Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;
36 Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,
37 Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.
38 Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.
39 Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon
40 don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.
41 Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
42 Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.
43 Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.